'Yan Acaba sun yi bore a Nijar

Niger zanga-zanga Hakkin mallakar hoto

A jamhuriyar Nijar rahotanni na cewa kura ta lafa a garin Tawa da ke arewa maso tsakiyar kasar, sakamakon wata zanga-zanga da 'yan kabu-kabu suka yi a ranar Talata.

Rikicin ya samo tushe ne bayan wani sabani da aka samu tsakanin wani dan sanda da dan acaba.

Dan acabar ne kawai ya samu rauni a boren, kuma babu wanda ya rasa ransa.

Sai dai 'yan sandan sun kama mutane da dama, a sanadiyar zanga-zangar.