Jonathan ya nada shugabannin taron kasa

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahalarta zasu iya tattauna komai banda batun raba kasa

Gwamnatin Najeriya ya bayana tsohon babban mai sharia na kotun kolin kasar, Idris kutigi a matsayin jagoran babban taron kasa, da za'a yi nan ba da dadewa ba.

Shugaba Jonathan ya kuma nada tsohon ministan harkokin waje, Farfesa Bolaji Akinyemi a matsayin mataimakin shugaban babban taron yayin da Dr. Valerie Azinge ce sakariyar babban taron.

A cikin wata sanarwar da offishin Sakataren gwamnatin ya fitar ya ce shugabannin babban taron zasu fara aiki ne a ranar laraba a Abuja.

Gwamnatin kasar ta ce ana son wakilai 492 da zasu halarci taron, wanda ta ce za'a shafe watani uku ana mussayar ra'ayoyi akan abututuwan da suka shafi kasar.

Ya kuma ce bayan an kamala taron mahalata taron za su bada shawarwari akan matakan da gwamnati tarayya ya kamata ta dauka domin zartar da abubuwan da aka cimma zuwa doka.

Sai dai sakataren gwamnati Puis Anyim ya ce idan ba 'a cimma daidaito ba akan abubuwan da aka zartar a taron, za'a yadda da abubuwan da kashi 75 cikin dari na mahalarta taron suka amince da su.