Ba za mu tura soji Ukraine ba - Putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr. Putin ya ce tura soji Ukraine zai zamo mataki na karshe

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce babu bukatar tura sojojin Rasha cikin Ukraine a halin yanzu, a wani taron manema labarai a Moscow.

Ya bayyana cewa a Ukraine an yi wani juyin mulki wanda kundin tsarin mulki bai yarda da shi ba.

Mr. Putin ya kara da cewa Rasha ta amsa kiran hambararren shugaba Viktor Yanukovych ne, wanda ya nemi Rashar ta kare masu magana da harshen Rashanci dake zaune a Ukraine.

Kuma ya ce babu wata alaka dangane da abin dake faruwa a Ukraine da kuma sojojin da Rashar ta zuba a bakin iyakarta da Ukraine.