Shari'ar 'yan jarida a Masar

Masu zanga-zangar nuna goyon baya ga 'yan jarida
Image caption Lawyan 'yan jaridar ya ce tuhumar da ake ma su ba ta da karfi

A karon farko babban mai bincike a shari'ar da ake yi a Masar ta 'yan jarida 3 daga gidan talabijin na Al Jazeera ya bayyana a gaban kotu.

Ana zargin 'Yan jaridun da laifin yada labaran karya da kuma taimakawa kungiyar yan uwa musulmi, wadda hukumomin Masar suka ce kungiya ce ta yan ta'adda.

Mai binciken ya ce Shugaban ofishin Aljazeera a Masar, Mohammed Fahmy, dan kungiyar 'yan uwa musulmin ne saboda yana taimawa wata tashar TV dake watsa labaran dake amfanar kungiyar.

Wani lauyan wadanda ake kara , Farag Fathy, ya ce shedar ta yau ta nuna cewar tuhumar da ake yiwa 'yan jaridar 3 ba ta da karfi.

'Yan Jaridar sun yi kururuwar cewar su fursunonin siyasa ne, yayinda aka kawo karshen zaman ranar na sauraren karar.

Karin bayani