Boko Haram: An rufe makarantu a jihohi 3

Hakkin mallakar hoto Getty

Gwamnatin Nigeria ta sanar da rufe kwalejojinta dake jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe saboda barazanar tsaro da ake fuskanta a wadannan jihohin.

Makarantun da aka rufe sun hada da: Kwalejin 'Yan mata ta tarayya dake Munguno, da Kwalejin kimiyya da fasaha dake garin Lassa a jihar Borno, da kuma Kwalejin 'Yan mata ta tarayya dake Potiskum, da Kwalejin tarayya dake Buni Yadi a jihar Yobe, da kuma kwalejin kimiyya da fasaha dake Michika a jihar Adamawa.

Sanarwa daga ofishin ministan ilimi, Nyeson Wike ta ce, an dau wannan mataki ne domin kare rayukan dalibai.

Cikin 'yan makonnin da suka gabata ne dai 'yan Boko Haram suka kai hari a kwalejin tarayya dake Buni Yadi inda aka kashe dalibai 29.

An kuma ƙona makarantar ƙurmus.

Wannan dai ya jefa fargaba ga masu zuwa makaranta a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Koda a baya an sha kai hare-hare a wasu makarantun a jihohin Borno da Yobe