Bauchi: An yiwa 'yan luwadi 4 bulala

Hakkin mallakar hoto

Rahotanni daga Bauchi a arewacin Nijeriya na cewa, an yiwa wasu mutane huɗu bulala a bainar jama'a bayan kotun shari'ar musulunci ta same su da laifin aikata luwaɗi.

Mutanen da aka yanke wa hukuncin matasa ne 'yan shekarun da suka kama daga 20 zuwa 22, kuma an kwantar da su ne a bainar jama'a kana aka yaye riga ta baya aka yi musu bulala.

An ɗage shari'ar mutanen a watan Janairu saboda gungun wasu matasa sun aukawa kotun inda suka nemi a ba su damar su ladabtar da mutanen.

Alkalin da ya yanke hukuncin ya ce, ya sassautawa matasan 4 hukunci ne saboda a da ne suka aikata luwaɗin kuma sun yi alƙawarin ba zasu sake aikatawa ba.

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya sanya hannu akan wata doka ta haram auren jinsi guda da kuma luwaɗi da maɗigo.