Nigeria: An daƙile kai hari Ajiri da Mafa

Hakkin mallakar hoto AP

Hedikwatar tsaron Nigeria ta ce, cikin daren jiya sun katse yunƙurin 'yan Boko Haram na kai hari a ƙauyukan Ajiri, da Mafa a jihar Borno.

Wata sanarwa daga hedikwatar tsaron kasa dauke da sa hannun Manjo Janar Chris Olukolade ta ce, dakarun Nijeriya sun kashe 'yan Boko Haram 20, kuma soja sun samu raunuka.

Dakarun Nijeriyar sun kuma ce sun lalata sansanonin 'yan Boko Haram dazuka da kuma cikin tsaunuka dake jihar Adamawa da kuma Borno.

Sojan Nijeriyar sun kuma ce, sun kwace makamai da dama daga 'yan Boko Haram.

Sai dai kuma hedikwatar tsaron ta bayyana takaici dangane da abinda ta kira kalamai na kashe gwiwar soja da wasu manyan mutane suke yi.

Sun kuma ce, ko alama 'yan Boko Haram ba su fi karfin sojan Nijeriya ba.