Nigeria: Gusau ne sabon ministan tsaro

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Goodluck Jonathan, shugaban Nijeriya

Shugaba Goodluck Jonathan ya nada sabbin ministoci goma sha ɗaya da suka haɗa da Aliyu Gusau ministan tsaro, Aminu Wali shi ne sabon ministan hulɗa da ƙasashen waje, Lawrencia Laraba ita ce ministar kula da muhalli.

Boni Haruna shi ne ministan kula da matasa, Asabe Asama'u Ahmed ce ministar aikin gona, Akon Eyakenyi ita ce ministan kasa da muhalli, an kuma nada Abduljelili Adesiyan a matsayin ministan harkokin 'yan sanda.

Sauran ministocin sun hada da Musiliu Obanikoro minista a ma'aikatar tsaro, Muhammed Wakil minista a ma'aikatar makamashi, Khaliru Alhassan minista a ma'aikatar lafiya.

A yau din kuma shugaba Jonathan ya cire ministan wasanni, Bolaji Abdullahi, inda nan take aka maye gurbinsa da Tamuno Danagogo.

Hankali zai fi karkata ne ga ministan tsaro, Aliyu Gusau ganin irin kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, inda cikin wannan watan kadai an kashe mutane fiye da 200.