Nigeria: An kashe mutane 11 a jihar Pilato

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya na cewa an kashe mutane akalla 11 a wasu hare-hare a kanannan hukumomin Riyom da Shendam yayin da wasu mutanen da dama suka samu raunuka.

Lamuran dai sun auku ne daga yammcin jiya zuwa kusan asubahin yau.

'Yan bindigar sun kai hare-hare ne a kauyuka hudu da suka hada da Gon, da Wereng, da Torok, da kuma Gwa-Rim.

An kuma kona kauyukan lamarin da ya tilastawa mutane gudu domin tsira.

Jami'in tsare-tsare na kungiyar agaji mai zaman kanta ta Stefanos Foundation, Injiniya Mark Lipdo, ya tabbatar da cewa an kashe mutane 11 ne kuma mutane tara cikinsu, an ƙona su ne a gida ɗaya a ƙauyen Gon.

Shi ma wani tsohon dan majalisar dokokin jihar filato, Emmanuel Danboyi Jugul, ya shaidawa BBC cewa ana ci gaba da zaman fargaba da zullumi a ƙaramar hukumar Riyom.

Jami'an tsaro na soja da 'yan sanda ba su ce uffan ba dangane da wannan lamari.