Saudi, Bahrain da UAE sun yanke hulɗa da Qatar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masar ta na takun saka da Qatar

Saudi Arabia da daular tarayyar larabawa UAE da kuma Bahrain sun janye jakadunsu daga kasar Qatar domin nuna rashin jin dadinsu da abinda suka kira katsa landan a harkokinsu na cikin gida.

A wata sanarwar hadin gwiwa kasashen uku sun ce, Qatar ta ki aiwatar da yarjejeniyar tsaro ta kungiyar hada kan kasashen yankin Gulf da sarkin Qatar, Sheik Tamim Al Thani ya sanyawa hannu cikin watan Nuwambar bara.

Kasashen uku sun kuma zargi Qatar da ƙin kaucewa yin katsa landan a harkokin cikin gidansu.

Sun kuma zargi Qatar da tallafawa kafofin yaɗa labarai masu sukan su.

Tashar talabijin ta Al Jazeera wacce gidan sarautar Qatar ce ke mallakar ta na sukan gidajen sarautar Saudi Arabia da kuma wasu kasashen yankin Gulf.