Mutane su rage shan zaƙi -inji WHO

Hakkin mallakar hoto PA

Hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO ta ce, domin kiyaye lafiya ya kamata jama'a su rage yawan zaƙin da suke sha kowacce rana.

Hukumar ta kuma ce, ya kamata mutane su rage yawan shan zaƙin da ake samu a cikin zuma, da magunguna, da ruwan kayan marmari da ake kira 'juice' a Turance.

Sai dai masu yaƙi da yawan shan zaƙi a nan Birtaniya sun ce, abin takaici ne sai yanzu hukumar lafiya ta duniya ta ke magana akan illar shan zaƙi da yawa.

Sun kuma ce, ai kamata yayi a ɗau wannan mataki tun shekaru gamo da suka gabata.

Wasu masana lafiya sun danganta karuwar ƙiba da jama'a suke yi ga yawan shan zaƙi.

Likitoci suna danganta kamuwa da wasu cututtuka masu barazana ga rayuwa ga ƙiba.

Hukumar lafiya ta duniya dai dama ta bada shawarar cewa, kowacce rana zakin da mutum zai sha ta kowacce hanya kar ya wuce kashi goma.