NATO za ta sake duba dangantakarta da Rasha

Anders Fogh Rasmussen Hakkin mallakar hoto AP
Image caption NATO ta ce Rasha ta cigaba da keta 'yancin Ukraine

Sakatare Janar na Kungiyar tsaro ta NATO, Anders Fogh Rasmussen ya ce kungiyar na duba dukanin dangantakarta da Rasha saboda rikicin Ukraine.

Da yake magana bayan tattaunawa tare da jakadan Rasha a Kungiyar tsaron ta NATO, Mr Fogh Rasmussen ya ce, wannan ya hada har da dakatar da wani aikin hadin guiwa da ya shafi lalata makaman Syria masu guba, kodayake ya ce hakan ba zai shafi lalata makaman ba.

Ya ce Rasha ta ci gaba da keta 'yanci da martabar kasar Ukraine da kuma alkawurran da ta yi ga duniya.

A nasa martanin Jakadan Rashan, ya zargi kungiyar ta NATO da yin amfani da halayyar zamanin cacar baki a kan kasarsa.

A halin da ake ciki kuma, Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya bukaci takwaran aikinsa na Rasha, Sergei Lavrov, da ya gudanar da tattaunawar kai tsaye tare da gwamnatin wucin gadin Ukraine.

Karin bayani