Ghana ta kama 'yan china kan safarar mata

'Yan sanda a kasar Ghana Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan sanda a kasar Ghana

'Yan sanda a birnin Takoradi mai tashar jiragen ruwa a kasar Ghana, sun cafke wasu 'yan kasar China biyu, bisa zarginsu da safarar wasu mata bakwai.

Ana zargin mutanen biyu da sanya matan 'yan kasar Vietnam karuwanci a kasar ta Ghana.

Matan dai sun kwashe tsawon shekara kenan a kasar ta Ghana.

Bayanai dai sun nuna cewa mutanen sun dauko matan ne bayan da suka rude su cewa daga nan za su tura su Amurka domin samar musu ayyukan yi.