Taron gaggawa akan Ukraine

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai mabanbantan ra'ayi a kungiyar tarayyar turai akan Ukraine

Shugabannin Turai zasu soma wani taro na gaggawa domin yanke hukuncin yadda zasu maida martani game da jibge sojojin Rasha a Crimea

Wasu mambobin kungiyar tarayyar Turai musamman wadanda suka fito daga gabashin turai na son ganin an sanya takunkumi

Amma wasu karkashin jagorancin Jamus na bukatar a yi sulhu a matsayin hanyar warware rikicin.

Taron na Brussels na zuwa ne kwana guda bayan wata tattaunawa tare da Rasha a Paris wacce aka kammala ba tare da wata gagarumar nasara ba.