Nigeria: 'Soja sun kama 'yan Boko Haram'

Image caption Soja sun ce sun kama 'yan Boko Haram da dama

Dakarun Nijeriya sun ce, sun kama wani gwanin kisan mutane na kungiyar Boko Haram da suka ce, ya fadi cewa, shi ya kware ne wajen kashe mutane ta hanyar yanka da kuma sara.

Wata sanarwa daga hedikwatar tsaron Nijeriyar dauke da sa hannun Manjo Janar Chris Olukolade tace, a samamen da aka gudanar an kuma samu kama wasu 'yan kungiyar ta Boko Haram da suke taimakawa wajen bada bayanai.

Sanarwar ta kuma ce, dakarun dake aiki tare da rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa sun katse yunkurin 'yan Boko Haram na kai hari a wasu kasuwanni a kusa da Monguno da kuma New Marte.

Rundunar tsaron ta Nijeriya ta ce, ta ci gaba kai farmaki a wuraren da suka kafa sansanoni da kuma hanyoyin da suke bi.

Image caption Wasu sun yi korafin cewa, dakarun Nijeriya ba su da isassun makamai

Cikin 'yan makonnin nan 'yan Boko Haram sun zafafa kai hare-hare a sassa da dama na jihar Borno inda suka hallaka mutane da dama a garuruwan Maiduguri da Konduga, da Mainok da kuma Jakana.

Koda a jihar Adamawa 'yan Boko Haram sun kai hare-hare a garuruwan Michika da kuma kauyen Shuwa da ke karamar hukumar Madagali.

A wadannan hare-hare na jihar Adamawa an hallaka mutane fiye da 20.

Koda rundunar Sojin saman kasar ta ce ta na samun nasara a yakin da take yi da 'yan Kungiyar nan da ake cewa Boko Haram.

Sojan saman Nijeriyar sun ce, sun da kaddamar da hare hare ta sama a wasu sansanonin 'yan kungiyar a arewa maso gabashin Nigeria.

Saboda dalilai na tsaro gwamnatin Nijeriya ta rufe wasu makarantu a Adamawa da Borno da Yobe.