'Yan Boko Haram sun kashe matasa 7

Rahotanni daga Gwoza a jihar Borno na cewa akalla matasa bakwai ne wasu da ake zargin 'yan Boko Haram suka kashe da safiya yau akan hanyarsu ta zuwa kasuwa

Harin na zuwa ne bayan a ranar Larabar da ta gabata wasu maharan sun kai hari a garin Mafa jim kaɗan bayan ziyarar da gwamnan jihar Kashim Shettima ya kai domin yi musu jaje.

Hare-haren da ake kaiwa na daɗa haddasa tuɗaɗar mutane daga ƙauyuka suna guduwa birnin Maiduguri da kuma wasu garuruwan domin samun mafaka.

Cikin 'yan makonnin nan na kashe 'yan Boko Haram sun kashe daruruwan mutane a kauyukan jihar Borno.

Har yanzu jama'a suna rayuwa cikin firgici a wasu sassan jihar Borno.