ICC za ta yanke hukunci kan madugun yaki

Germain Katanga
Image caption Wannan ce shari'a ta farko da ta kunshi tuhume-tuhume kan lalata

Alkalai a kotun hukunta manyan laifukan yaki na duniya, ICC na gaf da bayyana hukunci a shari'ar da ake yi wa tsohon madugun 'yan tawaye na Congo, Germain Katanga.

Kotun na tuhumarsa ne da laifukan cin zarafin bil'adama.

Mai gabatar da kara ya ce Mr. Katanga ya jagoranci wani samame da aka kai da daddare a shekarar 2003, a kan kauyen Bogoro kusa da bakin iyakar Uganda.

Kimanin mutane 200 aka kashe, wasunsu kuma aka daddatsa a harin.

Tuhume-tuhumen da ake masa sun hada da fyade ga matan da ba a kashe ba, ko ajiye su domin yin lalata.