'Sauyin yanayi zai haifar da zazzabin cizon sauro'

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Sauro da ke dauke da cutar malaria na kara nisan kiwo idan yanayin dumi ya karu.

Masu binciken kimiyya a Birtaniya da Amurka sun ce sauyin yanayi zai haifar da yaduwar cutar zazzabin cizon sauro a fadin duniya zuwa yankin tuddan Afrika da Amurka ta Kudu.

Masanan sun ce karuwar dumamar yanayi za ta sa karin miliyoyin mutane su kamu da cutar ta zazzabin cizon sauro.

Binciken ya gano cewa sauro da ke dauke da cutar malaria na kara nisan kiwo idan yanayin dumi ya karu.

Sai dai mutanen da ke rayuwa a yankuna masu tudu ba su da kariya daga cutar, abinda zai sa ta yi saurin yaduwa.

Kimanin mutane miliyan dari biyu da ashirin ne ke fama da cutar zazzabin cizon sauro a fadin duniya.