Malaysia: Anwar zai yi shekaru 5 a jarun

Anwar Ibrahim Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Anwar ya jagoranci 'yan adawa, inda suka samu gagarumin nasara a zaben 2013 a Malaysia

Wata kotu a Malaysia ta yanke wa jagoran 'yan adawa Anwar Ibrahim, hukuncin shekaru biyar a gidan yari, bisa samunsa da laifin luwadi.

Kotun ta yi watsi da hukuncin wata babbar kotu wacce ta wanke shi, daga zargin yin luwadi da wani mai rufa masa baya a shekarar 2008.

Sai dai Anwar ya sha jaddada cewa zargin na da nasaba da siyasa.

Kotun ta ce Anwar zai iya cigaba da zaman beli, zuwa lokacin da zai daukaka kara zuwa kotun kolin kasar, a cewar kamfanin dillacin labarai na AP.

Kotu ta taba samun Anwar da laifin yin luwadi da direban matarsa a shekarar 2000, amma kotun kolin kasar ta wanke shi a shekarar 2004.