'Libya zata kone jirgin Korea ta Arewa'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawayen Libya na saida man kasar ga Korea ta Arewa

Firai Ministan Libya Ali Zeidan ya yi barazanar ya yi barazanar kone jirgin ruwan Koriya ta arewa da bom idan ya yi kokarin ficewa da man fetur daga wata tashar jirgin ruwa da ke gabashin kasar, wacce ke karkashin ikon 'yan bindiga masu neman a raba kasar.

Ya ce 'matukar jirgin ruwan ya ki bin umarnin, za mu yi masa luguden bama-bamai da zarar ya fice daga tashar kuma hakan zai iya haifar da mummunar barna ga muhalli'.

Ali Zeidan ya kuma ba da umarnin kama ma'aikatan jirgin ruwan.

Rahotanni sun ce ana loda man fetur din ne a tashar El-Sidr, daya daga cikin tashohin jiragen ruwan Libya guda uku da ke karkashin ikon masu neman a raba kasar.

Jakadan Amurka a Libya ya yi gargadin cewa duk wani kamfani da ke haramtaccen ciniki da 'yan tawayen zai fuskanci takunkumi daga kasashen duniya.