Soji sun kai wa kungiyar 'yan Hutu hari

Sojin Congo sun ce sun kai wa wani wurin da kungiyar FDLR ta 'yan kabilar Hutun Rwanda ke rike dashi.

Kakakin sojin, Olivier Amuli, ya ce an kashe dakarun gwamnati biyu da mambobin kungiyar biyu a wajen fadan, kafin 'yan tawayen su ruga cikin daji.

Da ma dai Majalisar Dinki Duniya na barazanar kai hari akan 'yan tawayen tun bayan da aka fatattaki kungiyar M23 a watan Nuwamba.

Sojin Congo sun ce sun kwace wurin daga hannun 'yan kungiyar FDLR, wanda ke kimanin kilomita 65 daga garin Goma, a ran Lahadi da safe.

Kakakin sojin ya ce dakarun Congon za su cigaba da yakarsu cikin 'yan kwanaki nan.

Wuyar ganewa

Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya gaya wa BBC cewa an tura dakarun majalisar su taimaki sojin Congon.

'Yan kungiyar FDLR dai sun wal-watsu ne a kudancin Congo -- da yawansu suna boye a daji, ko kuma sun shige cikin jama'ar gari -- abin da yasa gano su keda wuya sosai.

Kungiyar 'yan Hutun Rwandan sun zo Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo ne a shekaru 1990, bayan da 'yan tawayen Tutsi su ka kwace mulki a Rwandan.

An zargi wasu daga cikin mambominsu da laifin yin kisan kiyashi na Rwandan.

Kungiyar ta yi rauni sosai a cikin shekaru 20 da suka gabata saboda farmakin sojojin Rwanda da Kongo.

'Yan kungiyar sun nemi yin sulhu da gwamnatin Rwanda, amma gwmantin da Majalisar Dinkin Duniyar sun yi watsi da tayin nasu.