PDP ta ce Wammako ya nemi gafara

Shedkwatar jam'iyyar PDP a Abuja
Image caption Shedkwatar jam'iyyar PDP a Abuja

Jam'iyyar PDP mai mulki ta ce ya kamata gwamnan jihar Sokoto Aliyu Magatakdarta Wamakko ya yi karin bayani akan abun da yake nufi da shugaban kasa na gantali.

Mataimakin kakakin Jamiyyar Barista Abdullahi Jalo ya ce be jima ba da shugaba Gooduck Jonathan ya ziyarci jihohin Adamawa da Borno lokacinda aka yi wasu kashe-kashe.

Jam'iyyar ta ce zuwa wajen sarkin musulmi da shugaba Jonathan ya yi ba gantali bane kuma ya kamata gwamnan ya nemi gafarar fadar sarkin musulmi