Sojoji sun kammala rawar daji a Nijar

Taswirar Nijar
Image caption Taswirar Nijar

An kammala wani atisayen soji na kasa-da-kasa a Jamhuriyyar Nijar.

Amurka ce ta shirya atisayen tare hadin gwiwar wasu kasahen Afrika da Turai.

An shirya rawar dajin ne don koyawa dakarun Nijar din dana wasu kasahen Afrika dabarun tunkarar ta'addanci.

Ministan tsaron Nijar Mahamadou Karidio ya shaidawa BBC cewa "yaki da ta'addanci ya zama dole"