Boko Haram: Soji sun kutsa dajin Sambisa

Image caption Ana zargin 'yan kungiyar Boko haram da kai hare-hare a garuruwa da kauyuka a baya-bayan nan

Dakarun Najeriya sun ce sun samu kutsa wa cikin dajin Sambisa, inda ake kyautata zaton nan ne maboyar 'yan kungiyar da aka fi sani da Boko Haram.

Wani wanda ya je dajin Sambisan ya shaida wa BBC cewa ya ga motoci da dama da aka kona, da gawawwaki na mata da maza a can.

Hakan zuwa ne a lokacin da rahotanni ke cewa hafsan hafsoshin sojin kasar ya koma Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Watanni goma kenan da aka kafa dokar ta baci a arewa-maso-gabashin kasar, amma kawo yanzu jama'a na ganin ba a kai ga kawo karshen wannan matsala ba.