Malaysia: An faɗaɗa neman jirgi

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumomin Malaysia sun yanke shawarar fadada kokarin gano jirgin fasinjan da ya bata, awa guda bayan ya tashi daga birnin Kuala Lampur zuwa Beijing, babban birnin China.

Kwanaki uku bayan batan jirgin, duk da kokarin hadin gwiwa na kasashe da dama, har yanzu ba alamar jirgin.

Tuni dai China, wadda mutanenta ne suka fi yawa a cikin jirgin, ta bukaci hukumomin Malaysia da su kara azama domin gano jirgin.

Da dama daga cikin iyalai sun baiyana bacin rai saboda rashin sanin cikakken halin da ake ciki.