Arewa za ta fitar da matsaya kan taron kasa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Arewa House- Gidan Margayi Premier, Sir Ahmadu Bello

Kungiyar dattawan arewacin Nigeria mai suna Northern Elders Forum ta soma taro a birnin Kano don fitar da matsaya kan bukatun yankin lokacin babban taron kasa a za a fara makon gobe.

Taron wanda ya samu halartar jama'a da dama daga sassana arewacin kasar zai tattauna matsalolin da yankin ke fuskanta, da kuma yadda ya kamata wakilai daga yankin su fuskanci taron.

A halin yanzu dai arewacin Nigeria na fuskantar matsalolin tsaro, da rashin aikin yi da kuma koma bayan ilimi.

Wakilai kusan 492 ne za su halarcin taron daga sassa daban-daban na kasar.

Gwamnatin Nigeria ta nada tsohon babban mai sharia na kotun kolin kasar, Idris kutigi a matsayin jagoran babban taron.

Wasu masu sharhi na gannin cewar taron ba zai iya warware ko da daya daga cikin matsalolin da talakawan kasar ke fuskanta ba.

Karin bayani