Zanga zangar kin jinin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta kudu

Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sudan ta Kudu

Dubban mutane suka gudanar da zanga zanga kin amincewa da Majalisar Dinkin Duniya a Juba babban birnin kasar Sudan ta kudu .

Masu zanga- zangar na zargin Majalisar da samarwa 'yan tawaye da makamai.

Masu zanga -zangar sun nemi wakiliyar Majalisar dake kasar watau Hilda Johnson akan ta yi murabus.

A ranar juma'ar da ta gabata ne gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce ta capke wasu makamai da aka sa cikin jerin ayarin motoci dake dauke da abinci.

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta musanta zargin,