Taliban ta yi barazana game da zabe

Image caption Wasu daga cikin 'yan Taliban a Afghanistan

Kungiyar Taliban a Afghanistan ta umurci mayakanta su yi amfani da karfi don hana gudanar da zaben shugaban kasar da za a yi a farkon watan Afrilu.

A wata sanarwa, kakakin Taliban ya ce 'yan kasar ta Afghanistan sun kauracewa zaben.

Kungiyar ta kuma bukaci malaman addinni a fadin kasar su fadakar da jama'a a kan cewar gudanar da zabe wata farfaganda ce ta Amurka.

Zaben da aka gudanar da Afghanistan a shekara ta 2009 an samu tashin hankali, inda 'yan Taliban su ka kai hare-hare a kan 'yan takara da masu kada kuri'a da kuma ma'aikatan zabe.

Karin bayani