Rikicin kasar Ukraine

Dakarun dake goyon bayan gwamnatin Rasha Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun dake goyon bayan gwamnatin Rasha

Dakarun dake goyon gwamnatin Rasha na cigaba da rike iko a yankin Crimea na kasar Ukraine ba tare da fuskantar da wata tirjiya ba.

Wani gungun mutane sun yi ta harbi sama lokacinda da suka yi kokarin kutsa kai cikin wani sansanin soji domin su kwace motoci dake ciki.

Da farko dai sojojin Ukraine sun maida martani akan harin sai dai a yanzu tutar Rasha ce aka saka cikin sansanin