Dangote, IDB zasu samar da aiki a Nigeria

Alhaji Aliko Dangote Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dangote ne mutumin da ya fi arziki a nahiyar Afrika

Hamshakin atttajirin nan na Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, ya bukaci hadin kai daga bankin Islama na raya kasashe, IDB wajen bunkasa harkokin da zasu samar wa mutane ayyukan yi, musamman a arewacin kasar.

Dangote ya yi wannan kiran ne, yayin da yake gabatar da kasida, a lokacin wani taro da bankin IDB ya shirya a Jeddah na kasar Saudi Arabia.

A cewarsa, za su hada kai domin koya wa mutane sana'o'i da kuma ayyukan gona.

"Daga Adamawa zuwa Taraba, Jigawa da Sokoto da kuma Kebbi zamu dauki mutane aiki su kusan dubu 200 tsawon shekaru hudu", Dangote ya bayyana.

A bara ne Dangote ya sanar da soma gina katafaren asibiti mai gadaje 1,000 a mahaifarsa jihar Kano.

Karin bayani