Sojoji sun cafke 'yan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption 'Yan Boko Haram sun ce shugabanninsu sun ce kowa ya yi takansa

Hukumomin tsaro a Nigeria sun tattabatar da cafke wasu da suka ce 'yan kungiyar Boko-Haram ne a arangamar da sojoji suka yi da su a jihar Borno.

Wuraren da jami'an tsaron ta ce an yi bata kashin sun hada da Dikwa da Cross-Kauwa da Kukawa da kuma Alagarmo.

Hedikwatar tsaron Najeriyar ta bayyana cewa sojojin kasar sun ci nasarar kame wasu da suke zargin cewa 'yan boko-haram ne wadanda suka yi kokarin tserewa daga sansanoninsu daban-daban da ke jihar Borno.

Wata sanarwar da Kakakin hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo-Janar Chris Olukolade ya fitar ta nuna cewa mafi yawan wadanda aka kama sun samu munanan raunuka sakamakon bude musu wuta da aka yi a sansanonin nasu.

Sanarwar dai ta bayyana cewa wadanda aka kama din na ba da hadin kai ga jami'an tsaro yadda ya kamata, saboda suna ba su bayanan da suka ce za su taimaka musu a gwagwarmayar da suke da 'yan kungiyar Boko Haram.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa wadanda aka kama din sun bayyana cewa malamansu sun umurce su da su watse kowa ya koma gida saboda aikin da suka taro dominsa ya kare.

''Yan Boko Haram sun watse'

Sanarwar ta tabbatar da labarin da BBC ta bayar a wata hira da ta yi da wasu da suka ziyarci wasu daga cikin sasanonin 'yan kungiyar bayan wata tsagaita wuta a dauki ba dadin da jami'an tsaro ke yi da 'yan kungiyar a dajin Sambisa ranar Litinin din nan, inda wani da ya gana da wani da aka raunata ya ce malaman nasu sun shaida musu cewa 'aikin Allah' ya kare kowa ya kama gabansa.

Kazalika sanarwar ta yi ikirarin cewa wadanda aka kama din na ci gaba da rokon jami'an tsaro da su yi wa Allah da Annabin su bar su cikin rayayyu, kada su halaka su, suna alkawarin cewa za su su ba su duk wani cikakken hadin kan da suke nema.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Dakarun Nigeria a dajin Sambisa

Sun kuma shaida wa jami'an tsaron cewa suna fama da masifar yunwa da sansanonin nasu, ga kuma ruwan boma-bomai da ake musu ba kakkautawa duk kuwa da yawan sauya sansani da suke yi da wannan wurin zuwa wancan, inda aka raunata musu mutanensu da dama kuma ba magani ballantana a yi musu jinya.

Sanarwar dai ta kara da cewa jami'an tsaro na ci gaba da kai farmaki a wurare daban-daban a wannan yanki da ke fama da rikici, don haka ne rundunar sojin Najeriyar ke gargadi ga wasu da ta ji labarin cewa na ziyartar wasu daga cikin sansanonin da aka kai wa hari a dajin Sambisa.

A cewar sanarwar irin wannan ziyara na da hadari, kasancewar kawo yanzu sojojin Najeriya ba su kammala aikin da suke yi a wannan wuri ba.

Karin bayani