Dole intanet ya kasance mai 'yanci - Tim

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Talata 11 ga watan Maris ne aka ciki shekaru 25 da kirkiro intanet

Wanda ya kirkiro hanyar sadarwa ta intanet (World Wide Web), Tim Berners-Lee ya yi kira da ayi wani kudurin doka na duniya da zai tabbatar da 'yancin intanet.

Mr. Lee ya bayyana hakan ne a bikin cika shekaru 25 da kirkiro hanyar sadarwar, inda ya ce masu amfani da yanar gizo na fuskantar karin sa ido daga gwamnatoci da kuma ma'aikatu.

Ya yi gargadin cewa, ba za a samu gwamnati mai zubin al'amuranta a faifai ba, idan babu hanyar sadarwar intanet mai 'yanci.

Inda ya kara da cewa yana da muhimmanci a kare manufofin da suka kai intanet ya cimma nasarorin da ya samu.