Mahara sun kashe mutane a jihar Katsina

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema

Rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriya sun ce an kai hare-hare a kananan hukumomin Sabuwa da Faskari, inda aka kashe mutane da dama.

Rahotannin sun ce tun karfe 12 na ranar Talata wasu mutane a kan babura da ba a san ko suwaye ba suka fara bin unguwannin kananan hukumomin suna bude wuta.

Kawo yanzu ba a san iya yawan mutanen da aka kashe ba, yayin da wasu da suka tsira ke cewa sun fi arba'in.

An kai wadanda suka samu raunuka asibitin Funtua, inda a can ma aka ce wasu biyu daga cikinsu sun rasu.

Karin bayani