Shin Nigeria na yaki da rashawa kuwa ?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Galibin 'yan Nigeria na kallon ana sace albarkatun kasa

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan na son duniya ta yi amanna cewar shi da gwamnatinsa suna yaki da cin hanci da rashawa.

Amma abubuwa biyu da suka faru kwanakin nan sun nuna cewar ba da gaske yake yi ba.

A lokacin da shugaba Jonathan ke bada kyautuka na bukin cikar Nigeria shekaru 100 da dunkulewa, wasu sun nuna rashin jin dadinsu game da baiwa tsohon shugaban kasar Sani Abacha kyauta.

A cikin makon da aka baiwa Janar Abacha wannan kyauta ne gwamnatin Amurka ta bada sanarwar gano wasu kudade kusan $458 da ta ce Abacha ya sace. Ana dai zargin Janar Abacha da sace kusan dala biliyan uku lokacin yana mulkin kasar.

Kakakin Shugaban kasar ya ce an baiwa Abacha kyaute ne saboda gudunmuwarsa ga hadewar kasar waje guda.

Amma shaharerren marubucin nan, Wole Soyinka wanda ya ki karbar irin wannan kyauta ya bayyana Abacha a matsayin "azzalumi wanda ya sace dukiyar al'umma".

'Na biyu'

Abu na biyu shi ne yadda Shugaba Jonathan ya dakatar da Gwamnan Babban bankin kasar, Sanusi Lamido Sanusi jim kadan bayan ya zargi kamfanin man fetur na kasar NNPC da kin saka $20bn na kudin danyen mai da aka sayar cikin asusun gwamnati.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dakatar da Sanusi Lamido saboda ya fasa kwoi

Koda yake wasu sun ce Malam Sanusi Lamido ya saka siyasa a cikin lamarin, amma da dama na ganin matakin a matsayin yunkurin rufe bakin gwamnan babban bankin saboda ya kunyatar da gwamnatin kasar a idanun duniya.

Bisa wannan zargin dai kenan ana sace kusan $1bn na danyen mai a a kowance wata a kamfanin NNPC a tsawon watanni 19.

Sanusi Lamido ya shaidawa BBC cewar yana fatar Majalisar Dattijjan kasar za ta gano gaskiyar lamarin game da wannan zargin.

'Badakalar Kalanzir'

Daga cikin zargin da gwamnan babban bankin Nigeria ya yi harda batun kudin tallafin kalanzir da aka ce gwamnati na yi wa masu kananan karfi a cikin kasar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Diezani Alison Madueke, Ministar man fetur a Nigeria

Sai dai a kashin gaskiya miliyoyin 'yan Nigeria ba sa samun wannan rangwame na farashin kalanzir.

Wata 'yar Nigeria Alimatu ta shaidawa BBC cewar "Muna sayen lita daya na kalanzir a kan naira 140 zuwa 160".

A cewarta bata san inda ake sayar da kalanzir a kan naira 50 kowace lita ba kamar yadda gwamnati ta ce tana tallafawa.

A lokacin binciken da kwamitin Majalisar Dattijan Nigeria ya gudanar, ministar harkokin man fetur, Diezani Alison Madueke ta karyata zargin da ake yi wa ma'aikatarta da kamfanin NNPC, kuma ta ce za su bada bayanai game da kudaden da ake cewa sun bace.

Wadannan abubuwan sun nuna cewar da kamar yuwa a hukunta masu sace dukiyar Nigeria.

Karin bayani