An cafke 'yan Niger 150 a Ghana

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dakarun tsaron Ghana

Jami'an tsaro a kasar Ghana sun cafke wasu 'yan kasar Niger su 125 bisa zarginsu da hakar zinare ba bisa ka'ida ba.

Wadanda aka cafken galibinsu matasa ne da shekarunsu suka kama daga 15 zuwa sama.

A wata sanarwa da ta fitar, Hukumar kula da shige da ficen kasar ta ce an cafke mutanen ne a wasu gidaje dake zangon garin Kibi a jihar gabashin kasar.

A cikin 'yan shekarunnan, gwamnatin Ghana ta matse kaimi wajen damke 'yan kasashen waje masu saba ka'ida wajen hako zinare a cikin kasar.

A baya an tsare 'yan kasar China da dama wadanda ke hako ma'adinan kasar ta Ghana ba bisa ka'ida ba.

Karin bayani