Tsohon Shugaban Saliyo Ahmad Kabbah ya rasu

Image caption Margayi tsohon Shugaban kasar Saliyo, Ahmad Tejan-Kabbah

Tsohon Shugaban kasar Saliyo, Ahmad Tejan-Kabbah ya rasu bayan doguwar jinya da yayi.

Mr Kabbah ya jagoranci kasar a lokacin da aka yi yakin basasa, kafin ya gayyaci dakarun Nigeria da na Birtaniya su fatattaki 'yan tawaye.

Ya sauka daga kan mulki a shekara ta 2007 bayan ya yi wa'adin mulki biyu da dokar kasar Saliyo ta tanada.

Mr Kabbah ya rasu yana da shekaru 82.