An kashe mutane 69 a Katsina

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Ana samun karuwar hare-haren 'yan bindiga a Nigeria

Rahotanni na baya-bayannan da muka samu daga jihar Katsina sun nuna cewar kawo yanzu an kashe mutane kusan 69 a hare-haren da aka kai a wasu kauyukan jihar.

Dan majalisar wakilan tarayya dake wakiltar mazabar Faskari da Kankara da kuma Sabuwa, Barrister Abbas Abdullahi Machika wanda ya shaidawa BBC yawan alkaluman mutanen da aka kashe ya ce "an yi jana'izar mutane 47 a Mararrabar mai gora, sai mutane 7 a Kuran mota ,wasu 7 a Unguwar rimi da kuma karin 8 a Mai gora".

Machika ya bayyana cewar wadanda aka kashe sun hada da mata da kananan yara da kuma maza.

A cewarsa ana ci gaba da dauko gawarwaki daga dajin Faskari.

Tun a ranar Talata ne wasu 'yan bindiga a kan babura suka bude wuta kan al'ummomin hukumomin Sabuwa da Faskari inda suka hallaka mutane tare da kona gidaje.

An kai wadanda suka samu raunuka asibitin Funtua, inda a can ma aka ce wasu sun rasu.

Kawo yanzu babu bayanai ba daga wajen jam'ian tsaron jihar Katsina, amma dai dan majalisar wakilan ya yi zargin cewar duk an kwashe jami'an tsaro an kaisu birnin Katsina don kare Shugaban kasar, Goodluck Jonathan wanda ke kai ziyara a jihar.

Karin bayani