Paparoma Francis ya cika shekara daya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Paparoma Francis na da farinjini a tsakanin kiristoci

Kiristoci mabiya darikar Roman Katolika na murnar zagayowar ranar da aka zabi Paparoma Francis a matsayin shugaban cocin.

Paparoma Francis, wanda a da ake kiransa Cardinal Bergoglio, dan kasar Argentina, shine Paparoma na farko daga yankin Latin Amirka.

Mabiya Katolika dayawa na da ra'ayin cewa, lafazinsa ya sha bamban sosai da na wanda ya gada, watau Paparoma Benedict.

A sakon da ya rubuta a shafinsa na Twitter, Paparoma Francis ya bukaci mabiyansa miliyan goma sha biyu, da su yi masa addu'a.

Ra'ayin jama'a a Italiya ya nuna cewa, Paparoma Francis ne ya fi farinjini daga cikin jerin Paparoman da aka yi a shekarun baya-bayan nan.

Karin bayani