Soji: An dakile harin Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Maiduguri na karkashin dokar ta-baci.

Rundunar sojojin Nigeria ta ce ta dakile wani hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka kaddamar a kan barikin sojoji na Giwa da nufin kubutar da 'yan uwansu da ke tsare a barikin.

A cikin sanarwar da ta fitar, wadda Manjo Janar Chris Olukolade ya sanyawa hannu, rundunar tsaro ta Nigeria ta ce, wasu tsirarun 'yan ta'adda, mai yiwuwa da nufin kara karfin mayakan da suka yi hasara, sun kaddamar da hari a kan wani barikin soji da ke Maiduguri da nufin kubutar da 'yan uwansu wadanda ake tsare da su.

Rundunar ta ce, sojoji sun samu nasarar dakile wannan hari, inda suka yiwa yan ta'addar mummunar barna ta hallaka mayakansu.

Kamar yadda sanarwar ta ce, wadanda aka hallaka a harbe-harben da 'yan ta'addar suka yi a kokarin da suke yi na kutsa kai inda ake tsare da abokansu, sun hada da wadanda suka yi kokarin kubutarwa.

Rundunar ta ce an kame da dama daga cikin wadanda suka kai harin tare da makamansu.

Sanarwar ba ta bayar da adadin yawan mutanen da aka hallaka ba, amma ta ce an jikkata sojoji hudu, wadanda yanzu haka ake yiwa magani.

Karin bayani