Boko Haram: Kamaru zata taimaki Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Kamaru ba zata kyale 'yan Boko Haram suyi amfani da kasar ta ba'

Kasar Kamaru ta ce ba za ta taba kyale masu tada kayar baya na kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram yin amfani da kasar ta wajen tarwatsa Nigeria ba.

Ministan cikin gida na Kamaru Emmanuel Reni ne ya bayyana hakan a lokacin da yake isar da sako na musamman daga shugaban kasar Kamarun Paul Biya zuwa shugaban Nigeria Goodluck Jonathan.

Wannan na zuwa ne bayan da wasu da ake zargin 'yan kungiyar ta Boko Haram ne suka kai hari a garin Maiduguri, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

A baya dai wasu masu lura da al'amura na ganin cewa tamkar Kamarun na dari-darin taimakawa Nigeria a yakin da take yi da 'yan Kungiyar Boko Haram din.