'Yan Boko Haram sun yi barna a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mutane sun mutu a jihar Borno a shekaru biyar na rikicin Boko Haram

'Yan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da wani gagarumin hari akan birnin Maidguri.

Rahotanni sunce jama'a sun kidime inda aka yi ta guje-guje saboda karar harbe-harben da suka ji.

Daruruwan yan kungiyar ne suka afkawa birnin na Maiduguri inda suka rabu kashi kashi zuwa sassa daban daban na birnin

Yayin da wasu suka kaddamar da hari akan barikin soji na Giwa wasu kuwa sun doshi jami'a ne da kuma sabuwar GRA

Wadanda suka ga abun da ya faru sun ce an bankawa wasu gidaje wuta.

A kwanakin baya dai sojojin Nigeria sun ce sun fatattaki 'yan kungiayr daga dajin Sambisa, maboyar ta 'yan Boko Haram tare da kama wasu 'yan kungiyar.