Ana binciken jirgin Malaysia a kogin India

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun kasa da kasa sun bazama don neman jirgin saman

Gwamnatin Malaysia ta tabbatar da cewa an fadada bincike zuwa tazarar yamma a kogin India a kokarin gano jirgin saman nan da ya bace tun ranar Asabar.

Ministan sufuri Hishammuddin Hussein yaki cewa uffan a kan wani rahoto na Amurka wanda ke cewa jirgin ya ci gaba da tafiya har tsawon sa'o'i bayan da aka daina jin duriyarsa.

Shugaban hukumar zirga-zirgar jirage Azharuddin Abdulrahman ya ce kasar ta Malaysia na aiki kafada da kafada da Amurka domin tantance ko akwai wani bayani ta naurar Satellite wanda zai taimaka domin gano jirgin.

Rundunar sojin Amurka ta tura wani jirgin ruwa dauke da jiragen helikopta domin ci gaba da binciken kamar yadda kakakin Fadar White House Jay Carney ya bayyana.

Karin bayani