Za a fadada binciken jirgi cikin tekun India

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin ruwan Amurka za su shiga tekun India domin lalubo jirgi

Jami'an Amurka da ke taimakawa a kokarin gano jirgin Malaysia da ya bace sun ce sababbin bayanan da suka samu sun sa su karkata akalar bincike zuwa ga tekun India.

Rundunar sojin Amurka ta tura wani jirgin ruwa dauke da jiragen helikopta domin ci gaba da binciken kamar yadda Kakakin Fadar White House Jay Carney ya bayyana.

Jay Carney ya ce 'Muna tallafawa Malaysia wurin binciko jirgin da ya bace domin gano abinda ya same shi, saboda kwantar da hankalin dangin matafiyan da yanzu haka su ke cikin damuwa'.

Har yanzu dai 'yanuwan fasinjojin dake cikin jirgin na cikin zaman zulumi.