Nijar za ta kai karar mujallar "Jeune Afrique"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An zargi Nijar da karbar kudade daga Libya

A jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ta ce za ta kai karar mujallar ''Jeune Afrique '' a gaban kotu bisa kazafin da ta ce ta yi mata.

Jaridar dai ta buga wani labari ne da ke cewa gwamnatin kasar Libya ta baiwa hukumomin Nijar dalar Amurka miliyan 20 domin su mika mata Saadi Ghaddafi, labarin da gwamnatin ta Nijar ta ce zargi ne mara tushe.

A ranar 6 ga wannan watan ne dai gwamnatin ta Nijar ta mika Sa'adi Ghaddafi ga hukumomin kasar ta Libya domin ya fuskanci shari'ah.

Nijar ta ce ta mika dan Marigayi Ghaddafin ne saboda ya saba ka'idojin da aka gindaya masa na neman mafaka a Kasar.