"Dakarun Nigeria na azabtar da jama'a"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Babbar jami'ar kula da hakkin bil adama, Navi Pillay

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dakarun tsaro Nigeria sun taka hakkin bil adama a fadan da suke yi da 'yan Boko Haram.

Babbar jami'ar Majalisar Navi Pillay ta shaidawa manema labarai a Abuja cewar sojojin Nigeria a lokacin yaki na kusan shekaru biyar da suka shafe suna yi da 'yan Boko Haram sun gallazawa jama'a tare da azabtarda mutane.

A cewarta sojoji sun yi kisan gilla sannan kuma sun tsare mutane ba bisa ka'ida ba.

Rikicin 'yan Boko Haram a Nigeria ya janyo mutuwar dubban mutane a arewacin kasar.

Karin bayani