France: Za a tilastawa direbobi fashin tukin kwana dai-dai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dokar za ta fara aiki a ranar Litinin

Gwamnatin Faransa za ta tilastawa direbobi fashin tukin kwana dai-dai a birnin Paris, a wani yunkuri na rage gurbatar yanayi.

Dokar za ta fara aiki a ranar Litinin ne, a karo na biyu tun shekarar alif da dari tara da casa'in da bakwai.

Ranar Asabar gwamnatin ta sanar da wannan dokar saboda gurbatar yanayi tsawon kwanaki biyar a jere, a birnin Paris da kewaye.

Matsanancin sanyin da ake da daddare tare da zafi da rana ne suka hana hayakin da motoci ke fitarwa ya samu damar bajewa, abinda ya haddasa gurbatar yanayin.