An kashe mutane sama da 100 a Kaura Kaduna

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Wani dan siyasa a jihar Kaduna da ke Nigeria ya ce an kashe fiye da mutane 100 tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da 'yan bindiga suka kai wasu kauyuka guda uku.

Dan majalisar dokokin jihar Kaduna, Yakubu Bitiyong ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun kai hari ne a karamar hukumar Kaura da ke kudancin jihar ranar Juma'a da daddare.

Ya ce ya ga konannun gawarwaki, kuma maharan sun kone gidaje da dama tare da yashe rumbunan abinci.

Mazauna kauyukan dai na tserewa saboda fargaba.

Karin bayani