Kashe na'urar jirgin Malaysia aka yi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirgin da ya bace sama da kwanaki bakwai har yanzu ba duriyar sa

Pirai Ministan Malaysia ya ce da gangan aka kashe na'urar sadarwar jirgin kasar, wanda ya bace a makon jiya dauke da mutane 239.

Mr Najib Razak ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya gudanar da safiyar Asabar, inda ya ce sun fahimci kaguwar da jama'a suka yi na samun bayani game da 'yan uwansu.

Ya kuma tabbatar da cewa yanzu akalar binciken ta karkata zuwa ga tekun India bayan da alamu ke nuna cewa an karkata akalar jirgin.

Sai dai bai tabbatar da rahoton da wani jami'in gwamnatinsa ya bayyana cewa fashin jirgin aka yi ba.