Nigeria:Mutane sun mutu wajen neman aiki

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Galibin matasan Nigeria na fama da matsalar rashin aikin yi'

A Nigeria akalla matasa goma ne suka mutu yayin wani yamutsi da aka samu a babban filin wasanni na Abuja, inda aka shirya jarrabawar daukar ma'aikatan hukumar shige da fice.

Ma'aikatan kiwon lafiya sun ce, an kai da dama da suka jikkata zuwa babban asibitin gwamnatin Nigeria dake Abuja da kuma na Garki, amma ba su san yawan mutanen da suka mutu ba.

Rahotanni sun ce an samu irin wannan yamutsi a jahohin Kano da Gombe da kuma Benue da kuma Minna.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane 56,000 suka taru a filin wasa na Abuja domin wannan jarrabawa.

Ayi bincike

Jam'iyyar PDP a Nigeria ta nemi a gudanar da bincike game da mutuwar masu neman aikin hukumar shige da fice a Abuja.

A wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam'iyyar Chief Olisa Metuh a ranar asabar, PDP tace ta kadu matuka game da rahotannin asarar rayukan.

Jam'iyyar ta PDP ta kuma bukaci hukumomin gwamnati da su tashi tsaye wajen samar da ayyukan yi a Kasar.