Ana kuri'ar raba gardama a Crimea

Kuri'ar raba gardama a Crimea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kuri'ar raba gardama a Crimea

Ana kada sama da kashi hamsin cikin dari a kuri'ar raba gardamar da zata fayyace makomar yankin Crimea.

Kasahen yammacin duniya sun soki wannan kuri'ar raba gardamar.

Sabuwar gwamnatin Crimea mai goyon bayan Rasha ce ta shirya kuri'ar raba-gardamar.

Kuri'ar ta bai wa al'ummar yankin Crimea miliyan biyu zabin hadewa da Rasha ko kuma samun cin gashin kansu cikin Ukraine.